
Mijin Kwaila by Bilyn Abdul
MIJIN 'KWAILA ����♀
sabon salo daga labarin zahra adam ishaq
"-chapter one-"
Ahankali yake tafiya da motar sakamakon yanda ya iske saitin bakin makarantar yaran yacika yakuma batse da dandazon yaran da'aka riga aka taso daga makaranta,ya d'anja gajeren tsoki lokaci guda yana kallon tsadadden agogon dake hannunshi ya taka burki kamar yanda sauran masu ababen hawa y'an uwanshi sukaja nasu burkin sakamakon dakatar dasu da yellow piper yayi.
Ranshi 'kwarai yana a dagulene koda yake ba abin mamaki bane ganin fuskar tashi babu walwala kusan dukkan na tare dashi sunsan dahakan duk da yake mutum mayen barkwanci lokaci kankane yakoma kamar wani horror abin tsoro ga kowa saboda yanda yakecin magani kullum idanunshi suna manne da farin gilashi saboda yanda ya matsama idanun nashi da kuka wanda har yazuwa yau d'innan yakasa dena kukan,
Baya zato ko tunanin zaidena kukan rasa jigon rayuwarshi dayayi a cikin watanni shidda dasuka gabata.
Yazuwa wannan lokacin yazama abin tausayi ga kowa to ai dolene dukkan mai imani ya tausayama d'an sangirin saurayin maicike fal da 'kuruciya akan fuskarshi da dukkan sassa na jikinshi,
Rashi yayi babba rashin dayake ganin bazai ta'ba samun tamka ko madadin taba.ZAHRA ADAM ISHAQ cikakkiyar budurwar dasuka sha'ku tun yarinta shine yaci kashinta da fitsarinta ya goyata a gadon bayanshi yamata soyayya dabai ta'ba yima wani mahalu'ki a duniya irintaba rana guda ciwon mara yayi fatali da rayuwar zahara yazuwa barzahu,
Adai dai lokacin da yarage saura kwana uku rak!
Daurin aurensu,
Yashiga rud'u mara misaltuwa dayawa yawa anzata ya haukace,amma dayake allah gafurune kuma rahimu saiya tashi kafad'unshi yakuma saka mashi dangana duk da ikirarinshi na dena kallon kowacce y'a mace da gashi tunda yarasa zahra.
Y'amma dayawa sunsha kawo kansu gareshi wasu iyayensu zasu kawo talla wasu text zasumai amma haryau baiga mai maye gurbin zahra ba,
Yashafi gefen fuskarshi daya tuna aneesa wacce tanace mashi kamar chewing gum saboda so,
D'iyar 'kawar mummy ce,
Ya girgiza kai batare daya ankare ba.
Kamar ance dashi ya kalli gefen damarshi ya hangota cikin dandazon yara sa'anninta kamar sauran yara akwai uniform bulu da farin hijabi jikinta sai y'ar jakar makaranta saqale a hammatarta,
Wata mummunar fad'uwar gaba ta riskeshi lokaci guda ya cire gilashin fuskarshi yasake murza idanu gabanshi na bugun goma goma,
Dai dai lokacin data tsallako gefen dayake yara sun ragu sosai,
Tana tafe tana tsokanr yaran dake gefe da ita.
Caraf idanunta suka sar'ke cikin na ishaq wanda tuni anbasu hannu amma tsabar kallonta baimasan anbasu hannunba.
Tarin ababen hawa dasuke bayanshi suka addabeshi da horn hakan yasakashi waigawa da sauri, lokacin wani har yayi mashi overtaken yana fad'in "amma kai wawane,idan kallon mata kazoyi toka bamu hanya mu wucewa zamuyi "
Ishaq bai tankaba yagyara parking mota zuciyarshi kamar zata tsage saboda tashin hankali.
Ganin ita yaketa kallo yasata cewa da 'kawayenta"ummilolo kukalli d'an 'kauye yanata kallona kutsaya kuga yanda zanmashi gobe bazai sake kallonaba,ummana tace mai kallon mutane mayene."
Saita lalla'ba kamar zata wuceshi sai dai tana zuwa saitinshi inda ya sauke glassa d'in motar ta tofa yawu, cikin sa'a kuwa ya sauka akan fuskarshi.
Sauran students y'an uwanta suka saki baki suna kallonta duk sun kasa tafiya,
Yayinda su ummilolo suka hau tsalke suna kyalkyala dariya.
Itama dariyar take don asukwane tabar wajen da gudu,
Tana zuwa tami'kama su ummilolo hannu suka tafa, kafin tacigaba dayima ishaq gwalo tanasaka hannayenta saitin kunnuwanta almar eho…ya numshe idanu yana tunano zahranshi a irin wannan lokacin tayi makamancin hakan gareshi, lallai batada maraba da zahra, hannu yasaka ya lakace miyon,ya sumbata zahra daban take, komai nata so yakeyi.
Bai ankareba ya hango zahra can kusa dawani matashi irin masu tallar agwaluma d'innan,
Ta mararaice fuska tace dame agwaluma "kai don Allah bani d'aya?
Me agwaluma cikin mamaki ya kalleta yace"kibada kud'i sai abaki agwaluma yammata."
Sudai su ummilolo sun 'kunshe baki sunason dariya suna tsoron bala'in zahra don sunsan akwai daru.
Ta murgud'a wa mai agwaluma baki,"nace kabani d'aya kawai."
Me agwaluma ya fusata yace"tunda ubanki yabani jari meze hana inbaki d'aya."
Tazaro idanu"la la la..kazagi ubana?
Popular articles
Oct 05, 2025 04:08 PM
Oct 05, 2025 03:53 PM
Oct 05, 2025 08:21 PM
Oct 06, 2025 03:51 PM
Oct 05, 2025 08:27 PM
Comments (0)